11 Oktoba 2021 - 12:50
Najeriya: ​Shugaba Buhari Ya Yi Alkawarin Samar Da tsaro Ga ‘Yan Najeriya A Duk Inda Suke A Kasar

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a wajen bukin yaye daliban makarantar koyon aikin Soja, ta NDA a Kaduna. inda ya kara da cewa abin da gwamnatinsa ta sa a gaba yanzu shi ne ganin ta samar da tsaro ga ƴan Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Buhari ya kara da cewa : “gwamnatin sa ta siyo muhimman kayan aiki daga kasashen waje, da za a yi amfani da su wajen ragargaza yan ta’adda, mahara, yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da duk wanda ya ke yunkurin ta da zaune tsaye a fadin kasar.

A karshe ya yabawa shugaban makarantar, Ibrahim Yusuf kan yadda ya gyarata da kuma kawata ta ta yadda ko ina a duniya ana alfahari da ita.

Buhari ya isa garin Kaduna tun ranar Juma’a. Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tare da manyan jami’an gwamnati a jihar suka tarbe shi a filin jirgin saman Kaduna.

342/